Wasu ‘yan ƙungiyar sa-kai ta ƙasa a jihar Nassarawa sun yi nasarar kama mutane shida da ake zargi masu garkuwa da mutane ne a maɓoyarsu.
‘Yan Vigilante ɗin sun kai farmakin ne maɓoyar tasu da ke Tudun Waya tare da ceto mutane 7 da aka sace.
Waɗanda aka kama ana zarginsu da ayyukan garkuwa da mutane a kan hanyoyin Akwanga da Nasarawa Eggon da Lafia.
Inda aka miƙa su ga hukumar ‘yan sanda da ke Lafia domin zurfafa bincike da kuma girbe abin da suka shuka.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan na jihar Nassarawa, DSP Ramhan Nansel, ya ce ba zai iya tabbatar da faruwar al’amarin ba a haɗin da ake ciki, saboda yana jiran samun tabbataci.
Mazauna wannan gari sun yaba ‘yan Vigilante ɗin a yayin da suka fito domin gane wa idanunsu waɗanda ake zargin.