Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Muhammad Bin Salman ya jagoranci taro da manyan jami’an gwamnatocin ƙasashen duniya da ke halatar aikin hajji.
Taron – wanda Sarki Salman ke gudanarwa shekara-shekara – na samun halartar manyan jami’an gwamnatocin ƙasashen duniya da hukumomin gwamnati, da shugabannin hukumomin alhazai.
Jaridar Saudi Gazzet ta ruwaito cewa ganawar wadda a ka yi a fadar Sarkin da ke birnin Makka, ta samu halartar sarkin Malaysia Al-Sultan Abdullah Ri’ayatuddin Al-Mustafa Billah Shah, da shugaban ƙasar senegal Macky Sall, da shugaban Pakistan Arif Alvi, da shugaban Bangladesh Mohammed Shahabuddin,da mataimakin shugaban ƙasar Maldives Faisal Naseem, da Firaministan Masar Dr. Mustafa Madbouly.