Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan a Jama’iyyar ADC

A yau Litinin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, zai yankin kati domin shiga Jam’iyyar ADC a hukumance.

Manyan hidiman Atiku sun shaida wa Aminiya cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin yin rajistar Atiku a mazaɓarsa ta Jada 1 da ke Ƙaramar Hukumar Hada  ta Jihar Adamawa.

Atiku ya yi nuni da wannan mataki ne a wani taro da ya gudanar da shugabannin ADC na Jihar Adamawa a Yola, inda ya ce:  “A Najeriya gaba ɗaya akwai sabon motsi na siyasa, ko ba haka ba? Yau wannan motsi ya kai mu ina? ADC. Don haka, jama’ar Adamawa da Najeriya, jam’iyyarmu yanzu ita ce ADC, shugabanninmu kuma suna nan a zaune.”

Ya ƙara da cewa:  “Bayan haka, a ranar Litinin zan kasance a hukumance cikin ADC. Kafin yanzu ban shiga ba; ku ne kuka riga ni. Za ku karɓe ni?”

Tun da farko ana ta shakku kan irin jajircewar Atiku da kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Lam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, ga ADC, bayan da ƙungiyar adawa da suke jagoranta ta amince da jam’iyyar a matsayin dandalin ta na zaben 2027.

Rashin halartar Atiku da Obi wajen ƙaddamar da sabuwar hedikwatar ADC a makon da ya gabata ya ƙara haifar da tambayoyi kan ko suna nan daram da matsayar ƙungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *