Yau majalisar Najeriya za ta yi zaman gaggawa kan gyaran dokar zaɓe

A yau ne ake sa ran majalisar Najeriya za ta yi zaman gaggawa kan gyaran dokar zaɓe, yayin da matsin lamba ke ƙara ƙaruwa kan ‘yan majalisa su amince da wajabcin tura sakamakon zaɓe ta na’ura kai tsaye daga rumfunan kaɗa ƙuri’a yadda mutane za su iya gani.

Zaman gaggawar ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da kira daga jama’a da ƙungiyoyin farar hula da jam’iyyun adawa, waɗanda ke neman a saka tilasta tura sakamakon zaɓe kai tsaye a cikin gyaran dokar zaɓen da ake ci gaba da tattaunawa a kai.

Majalisar dattawa ta dakatar da zamanta na tsawon makonni biyu a ranar Laraba da ta gabata, bayan ta amince da ƙudirin gyaran dokar zaɓe, domin bai wa ‘yan majalisa damar tattaunawa da shugabannin ma’aikatun gwamnati da hukumomi da sassan gwamnati kan kare kasafin kuɗin shekarar 2026.

Sanarwar kiran zaman gaggawar na kunshe ne a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 8 ga watan Fabrairu, wadda aka rarraba wa sanatoci wanda magatakardar majalisar dattawa, Emmanuel Odo ya sanya hannu a takardar.

A cikin wasiƙar, Odo ya ce ya ɗauki matakin ne bisa umarnin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Duk da cewa an yi gyare-gyare da dama a cikin dokar, hankalin jama’a ya fi karkata ne kan wani sashe da ya haifar da ce-ce-ku-ce, wato ƙin amincewa da wajabcin tura sakamakon zaɓe ta hanyar na’ura daga rumfunan kaɗa ƙuri’a yadda mutane za su iya gani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *