Akalla rayukan mutane 85 sun salwanta ciki har da mata da yara yayin da wasu mutanen fiye da 320 suka ji munanan raunika bayan aukuwar wani turmutsitsi a birnin Sanaa da ke karkashin ‘yan tawayen Houthis na kasar Yemen.
Turmutsitsin ya auku ne a yayin da ake rabon taimako na kudade ga marasa karfi a wata makaranta da ke wata Unguwa da ake kira Bab el Yemen kamar yadda wani jami’in gidan asibitin dake karkashi ‘yan tawayen da ke da iko da yankin ya tabbatar.
Har kawo yanzu dai hukumomi ba su yi bayani ba kan musabbabin tirmimutsitsin mafi muni da aka samu a tarihin kasar, kana kuma ba su fitar da alkaluman wadanda lamarin ya ritsa da su ba.