Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa tana aiwatar da shirye-shirye da manufofin da za su bai wa ‘yan kasa damar yaki da kalubalen talauci da aikata laifuka da ta’addanci.
Shugaban ya ce shirye-shiryen da gwamnatinsa za ta bullo da su wani sabon salo ne na samar da tsaro.
A cewarsa, shirin zai kasance ne ta hanyar jajircewa wajen tinkarar kalubalen tsaro da ke yin barazana ga wannan kasa da ma yankin yammacin Afirka.Shugaba Tinubu ya kuma umarci duka shugabannin tsaro da su hada kai a kokarin da suke yi na kare martabar duka yankunan kasar nan.
Duka wadannan bayanai da shugaba Tinubu ya yi suna kunshe ne a cikin jawabinsa da mataimakinsa Kashim Shettima ya karanta lokacin da ya wakilce shi a wajen bikin kaddamar da horas da dalibai 70 a makarantar sojoji ta Nijeriya (NDA) dake jihar Kaduna a ranar Asabar.