• Home  
  • Za mu gina katanga a iyakokin Najeriya- Ministan tsaro
- Babban Labari - Labarai

Za mu gina katanga a iyakokin Najeriya- Ministan tsaro

Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya bayyana cewa yana da niyyar gina katanga a iyakokin Najeriya inda ya ce hakan zai taimaka wajen hana miyagun mutane shiga ƙasar. A hirarsa da BBC, Ministan tsaron ya bayyana cewa rashin tsaro a iyakoki na bai wa ‘yan bindiga damar tsallakawa cikin ƙasar daga ƙasashen da ke maƙwaftaka. […]

Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya bayyana cewa yana da niyyar gina katanga a iyakokin Najeriya inda ya ce hakan zai taimaka wajen hana miyagun mutane shiga ƙasar.

A hirarsa da BBC, Ministan tsaron ya bayyana cewa rashin tsaro a iyakoki na bai wa ‘yan bindiga damar tsallakawa cikin ƙasar daga ƙasashen da ke maƙwaftaka.

Ya ce katangar za ta taimaka wajen hana “miyagu” shiga sannan za su yi amfani da na’urori domin tsare wuraren da ba za a iya yin katanga ba.

“Watakila ba za mu iya samun katanga a ko’ina ba, saboda wasu wurare akwai ruwa inda ba za a iya gina katanga ba. Amma akwai fasaha da dama da za mu iya amfani da su cikin tsari. Wasu daga cikin waɗannan fasahar na iya kunna ƙararrawa da zarar an ƙetare iyaka, wanda zai ba mu damar daukar mataki nan da nan,” in ji Musa.

“Muna duba wannan al’amari daga kowane ɓangare.” in ji shi. Najeriya na da fiye da kilomita 4,000 na kan iyaka, amma ministan wanda ya taɓa zama shugaban Hafsan Sojojin Najeriya, ya ce gina katanga a dukkan iyakokin abu ne mai yiwuwa.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana sau da yawa cewa iyakokin ƙasar na daga cikin manyan dalilan ƙaruwar rashin tsaro.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000