An gurfanar da mutane 5 da ake zargi da kashe jami’in Civil Defense a Kano

Kotun majistiri mai lamba 4 dake zamanta, a unguwar Gyadi-gyadi ta bayar da umarnin tsare wasu mutane 5 a gidan yari kan zargi kashe jami’in hukumar Civil Defense reshen jihar Kano.

Wadanda ake tuhumar sun hada da Aminu Isah da kuma mutane 4, bisa zargin hada kai da farwa jami’in hukumar tsaron Civil Defense mai suna, AbduRauf Ali Ahmad Shariff, har suka halaka shi.

Lauyan gwamnatin jihar Kano kuma mai gabatar da kara Barista Auwal Usman Usman, ne ya gabatar da su, inda jami’in kotun Aminu Kurawa, ya karanto musu kunshin tuhumar wadanda suka musanta.

Sai dai lauyoyin wadanda ake zargin sun roki kotun ta basu belin wadanda suke karewa, inda lauyan gwamnatin jihar Kano ya roki kotun ta basu wata rana don kawo shawarwarin gwamnati.

Tunda farko ana zargin batagarin dauke da makamai inda suke yunkurin satar dunkiyar al’umma, lokacin da jami’in ya yi kokarin dakatar da su, har suka yi amfani da makamai suka jikkata sannan suka kashe shi.

Alkaliyar kotun Rakiya Lami Sani, ta dage ci gaban shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Fabarairun 2026, tare da bayar da umarnin tsare su a gidan yari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *