Kungiyar tallafawa marayu da marasa galihu ta SURE4U ta bayar da tallafin kayan abinci da suka haɗa da shinkafa da siga da mai.
An kuma rabawa mata atamfofi ɗai-ɗai kowannen su, kuma kudi Naira dubu biyar-biyar ga iyayen marayu 20, dake unguwar zoo road, a nan birnin Kano.
Babban limamin masallacin Hidayatu dake unguwar Zoo Road Malam Kamilu Inuwa, ya ja hankalin al’umma wajen tallafawa marayu. A nasa jawabin Wakilin Hukumar kula da safarar bil’adama ta NAPTIP Umar Farouk Muhammad ya ja hankalin iyayen marayu, da yaudarar su da ake yi wajen fitar da yaransu wasu ƙasashe da nufin neman kudi.
Da ta ke jawabinta a wajen taron shugabar gudanarwar gidan Rediyo da Talabijin na Muhasa Hajiya Aishatu Sule tayi kira ga iyayen marayu dasu ƙara haƙuri da juriya wajen baiwa ‘ya’yan su kyakkyawar tarbiyya ta yadda zasu zama masu nagarta a nan gaba.
Taron ya samu samu halartar shugabannin gudanarwar ƙungiyar, Sanata UK Umar Sarkin kibiya da shugabannin kwamitin unguwar, da sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu.