Home » Zan Farfaɗo da Tsarin Ilimi Kyauta, Lafiya, Tallafin Karatu – Abba Kabir Yusuf

Zan Farfaɗo da Tsarin Ilimi Kyauta, Lafiya, Tallafin Karatu – Abba Kabir Yusuf

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya yi sake yin alƙawarin fardaɗo da tsarin ilimi kyauta da kuma fannin lafiya kamar yadda tsohon gwamnan jihar Kano, Kwankwaso ya yi a zamaninsa.

Wannan jawabi ya fito ne ta bakin mai magana da yawun sabon gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa wanda ya ƙara da cewa gwamnan na kuma sane da samar da ruwan sha da ilimi da kuma ingantaccen tsarin lafiya.

Dawakin Tofa ya kuma tabbatar da cewa gwamnan a shirye yake ya farfaɗo da tsarin ilimin firamare da na sakandire kyauta tare da ba wa ɗalibai unifom kyauta da kayan koyo da abinci da kyakkyawan yanayi na koyo da koyarwa.

Haka kuma sabuwar gwamnatin za su biya wa ɗalibai jarrabawar kammala sakandire na WAEC da NECO tare da tsarin ƙarfafa wa malamai guiwa.

Har’ila yau, Ya tabbatar da cewa sabon gwamna ya yi alƙawarin farfaɗo da tsarin haihuwa kyauta tare da inganta asibitocin da ke faɗin ƙananan hukumomi 44 da jihar.

Da a ka tambaye shi game da batun ɗaukar nauyin karatun ɗalibai na gaba da sakandire, Sunusi Dawakin Tofa, ya tabbatar da cewa gwmnan ya yi alƙawarin zai farfaɗo da wannan tsari musamman ga fannin da suka shafi kimiyya da lafiya da injiniyarin a ƙasashen ƙetare.

Sannan ya tabbatar da cewa gwamnatin Abba za ta samar da kyakkyawan yanayi ga ‘yan kasuwa da kuma tallafi ga matasa da mata.

Abin jira dai a gani shi ne yadda sabuwar gwamnatin za ta cika waɗannan alƙawura da ta yi wa al’ummar jihar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?