• Home  
  • Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta bayyana Muhasa TVR a matsayin kan gaba wajen gyaran tarbiyyar al’umma.
- Babban Labari

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta bayyana Muhasa TVR a matsayin kan gaba wajen gyaran tarbiyyar al’umma.

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta Jihar Kano,ta kawo ziyara ta musamman gidan talabijin da radio na Muhasa, domin nuna goyon baya da kuma yaba kokarinsu wajen wayar da kan al’umma kan illar shan miyagun kwayoyi da sauran laifuka a fadin jihar. A yayin ziyarar, shugabannin kungiyar Dr. Muhammad Sunusi Balarabe, ya bayyana jin dadinsu kan yadda […]

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta Jihar Kano,ta kawo ziyara ta musamman gidan talabijin da radio na Muhasa, domin nuna goyon baya da kuma yaba kokarinsu wajen wayar da kan al’umma kan illar shan miyagun kwayoyi da sauran laifuka a fadin jihar.

A yayin ziyarar, shugabannin kungiyar Dr. Muhammad Sunusi Balarabe, ya bayyana jin dadinsu kan yadda gidan Radio da talabijin na Muhasa ke gabatar da shirye-shirye da suka shafi ilmantarwa da fadakarwa, musamman wadanda suka shafi matasa da kuma al’umma baki daya.

Shugaban ƙungiyar ya jaddada cewa, yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi ba na gwamnati kadai ba ne, na kowa da kowa don haka suka nemi hadin kan tsakanin kafafen yada labarai da kungiyoyi masu zaman kansu domin cimma nasarar wannan yaƙi.

A nata ɓangaren, shugabar gidan talabijin da radio na Muhasa Hajiya A’ishatu Sule, ta ce manufofin kungiyar sun yi daidai da na gidan radio da talabijin na muhasa, domin wanda ya assasa tashar burinsa ne na chanjawa tunanin mutane zuwa kyawawan dabi’u.

Ta ƙa da cewa shan miyagun ƙwayoyi na musamman tsakanin matasa na ƙara taɓarɓarewar tarbiya wanda ya zama wajibi masu ruwa da tsaki su yi duk abunda yakamata don daƙile matsalar.

Ziyarar ta kare ne da addu’o’i da kuma alkawarin ci gaba da hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu don inganta rayuwar al’umma.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000