Rundunar ƴansandan Jihar Kano ta sanar da daukar tsauraran matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya yayin bikin Takutaha na shekarar 2026, wanda za a gudanar a ranar Talata, 1 ga Satumba.
Kwamishinan ’yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa al’ummar jihar bisa yadda suke gudanar da bikin cikin lumana, hadin kai da bin doka a shekarun baya.
Bakori ya kuma gode wa sarakunan gargajiya, malaman addini, shugabannin al’umma, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki bisa hadin gwiwar da suke bai wa rundunar wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, rundunar ta ce ta tanadi matakan tsaro na musamman domin ganin an gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.
Matakan sun hada da gudanar da ayyukan leken asiri, sintiri na sa’o’i 24, binciken ababen hawa da mutane, da kuma tura jami’an tsaro na musamman da na sa ido zuwa wuraren da za a gudanar da bikin, hanyoyin shiga da fita da kuma wuraren da ake ganin za su iya zama barazana.
Kwamishinan ya gargadi ’yan daba da masu tada zaune tsaye da su nisanci wuraren bikin, yana mai cewa rundunar ba za ta lamunci tashin hankali, daba ko duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a ba.
Ya ce duk wanda aka kama yana aikata laifin karya doka za a gurfanar da shi gaban kotu domin fuskantar hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Rundunar ta kuma yaba wa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, kungiyoyin sa-kai da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Rundunar ta bukaci al’umma da su gudanar da bikin cikin lumana, su kasance masu bin doka, tare da gaggauta kai rahoton duk wani mutum ko abin da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa ko kuma ta layukan gaggawa na rundunar.
Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta yi fatan al’ummar jihar za su gudanar da bikin Takutaha cikin zaman lafiya, farin ciki da annashuwa
