Adadin danyen man da Najeriya ke hakowa ya ragu zuwa ganga dubu dari 9 da 99 a kowace rana a watan Afrilu, lamarin da y aba wa Angola damar shiga gaban Najeriya.
Ƙasar Angola na samar da gangar man fetur miliyan 1 da 63 a kowace rana.
Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton wata-wata da aka fitar a watan Afrilun makon da ya gabata na kungiyar kasashe masu arzikin danyen mai fetur.
Najeriya ta yi asarar gangunan danyen mai dubu 270 a watan Maris, kamar yadda alkalumman kungiyar OPEC din suka nuna.
OPEC ta ce gaba daya, mamboninta 13 na samar da gangunan mai miliyan 28 da dubu 60 a kowace rana a cikin watan da aka yi la’akari da shi wajen yin wannan rahoto.
Sannan rahoton ya ce an samu karuwar danyen man da ake samarwa a Sudiyya, Angola da Iran, a yayin da aka samu akasin haka a Iraq da Najeriya.