Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta ƙasa reshen jihar Kano ta taya sabon jami’in yaɗa labarai na gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Sanarwar taya murnar wacce ta samu sa-hannu ciyaman ɗin ƙungiyar kwamared Abbas Ibrahim da sakataren ƙungiyar kwamared Abba Murtala waɗanda suka ce an ajiye ƙwarya a gurbinta saboda irin ƙwarewa da yake da ita.
Ƙungiyar ta yi wa Sunusi Bature Dawakin Tofa fatan zai gudanar da ayyukansa cikin nasara.