• Home  
  • Ƙananan Hukomomin Kano 44 sun kare kasafin kuɗin 2026
- Babban Labari - Labarai

Ƙananan Hukomomin Kano 44 sun kare kasafin kuɗin 2026

Kwamitin ƙananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Kano, ya zauna da shugabannin ƙananan hukumomi 44, domin su kare kasafin kuɗin su na 2026 da su ka mika. Kwamitin wanda aka raba zuwa gida shida, ya gana da shugabannin ƙananan hukumomi daban-daban. Hakaazalika bayan kammala kare kasafin kuɗin na su a gaban majalisar, shugabannin sun bayyana […]

Kwamitin ƙananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Kano, ya zauna da shugabannin ƙananan hukumomi 44, domin su kare kasafin kuɗin su na 2026 da su ka mika.

Kwamitin wanda aka raba zuwa gida shida, ya gana da shugabannin ƙananan hukumomi daban-daban.

Hakaazalika bayan kammala kare kasafin kuɗin na su a gaban majalisar, shugabannin sun bayyana cewa, kasafin kuɗin na su na 2026, zai mayar da hankali wajen bunƙasa harkokin Ilmi da lafiya sai kuma ayyukan raya kasa.

Rahotanni na cewa ƙananan hukumomin sun gabatarwa majalisar adadin kasafin kuɗin da ya kai kimanin sama da Biliyan Goma kowace ƙaramar hukuma.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai