Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller Road, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a, Farida Dan-Baffa, ta yanke wa wani Matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsa da laifin kashe wani Matashi a lokacin wani bikin kidan DJ.
Tun da fari, an gurfanar da, Najiyullahi Alkasim, a gaban kotun bisa tuhumar kisan kai wanda ya saba da sashi na 221 na Penal Code.
Lauyan gwamnati mai gabatar da kara, Barista Lamido Abba Soran-Dinki, ya gabatar da shaidu hudu, yayin da wanda ake tuhuma ya kawo shaidu uku domin kare kansa.
- An Kama ’Yan Bindiga 4 A Kano
- Yan Sanda Sun Sake Jaddada Dokar Hana Achaba A Wasu Kananan Hukumomin Kano
A yayin yanke hukunci, mai shari’a, Farida Dan-Baffa, ta yi nazarin bayanan kotu, tare da tabbatar da cewa, hujjojin da aka gabatar sun isa wajen tabbatar da laifin. Saboda haka, ta same shi da laifi, ta kuma yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Lamarin ya faru ne a unguwar Dawakin Dakata da ke Kano, lokacin da ake gudanar da wani kidan DJ, inda rikici ya ɓarke. A cewar shaidu, wanda aka yanke wa hukuncin ya caka wa marigayin, Isyaku Yau, wata sukundiriba a wuya, lamarin da ya jawo rasuwarsa.
