• Home  
  • Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad Ya ce suna nema Jam’iyyar da za su shiga amma banda APC
- Babban Labari - Siyasa

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad Ya ce suna nema Jam’iyyar da za su shiga amma banda APC

Daga Muazu Hardawa, Bauchi Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Bauchi ta yunkura don bayyana matsaya game da tattaunawar siyasa da ta ke yi da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai Mulki a Nigeria, tana mai cewa an rufe babin tattaunawar gaba ɗaya bayan tashi baram baram. Cikin taron manema labarai da Shugaban jamiyyar […]

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Bauchi ta yunkura don bayyana matsaya game da tattaunawar siyasa da ta ke yi da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai Mulki a Nigeria, tana mai cewa an rufe babin tattaunawar gaba ɗaya bayan tashi baram baram.
Cikin taron manema labarai da Shugaban jamiyyar PDP na Jihar Bauchi, Pharmacist Sama’ila Burga, ya Kira ranar asabat 18/4/2026, yadda ya bayyana cewa jam’iyyar APC ce ta fara gayyatar Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, tare da ‘yan PDP da sauran zababbun shugabanni domin su shiga jam’iyyar mai mulki.
Samaila Burga ya ce, “Mun shiga tattaunawar ce da kyakkyawar niyya, domin girmama kowa da kuma mutanen da ke cikinta. Ya kara da cewa gwamnan da sauran masu ruwa da tsaki na PDP sun shiga wannan tsari ne domin inganta hadin kai da kuma duba abin da ya fi alheri ga Jihar Bauchi amma aka gaza daidaita sahun siyasar.

Ya bayyana cewa kafin daukar wannan matsaya, jam’iyyar ta yi tuntuba mai fadi da muhimman masu ruwa da tsaki, ciki har da ‘yan Majalisar Tarayya, ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi da kuma shugabannin kananan hukumomi.
A cewarsa, tattaunawar ta tsaya cik ne bayan bangarorin biyu sun kasa cimma matsaya kan muhimman sharudda.
Don haka Ya zamo wajibi a bayyana sharuddan da aka amince da su, amma yawanci ba su samu karbuwa ba daga shugabannin APC,” in ji Burga.
Saboda haka, Shugaban na PDP Samaila Burga ya tabbatar da cewa an dakatar da duk wata tattaunawa da APC, tare da jaddada cewa a halin yanzu babu wani shirin kulla kawance da jam’iyyar ta APC.
Ya ce tattaunawar ba ta haifar da sakamako mai gamsarwa ba, kuma an rufe ta babu wata nasara da aka cimma. Yanzu haka suna duba wasu jamiyyun siyasa don tattaunawa da ta fi alheri domin amfanin al’ummar jihar Bauchi da ci gaban siyasar jihar.
Alhaji Samaila Burga ya kara da cewa tattaunawa da aka yi da jamiyyar ADC a kwanakin baya har gwamna Bala Mohammed ya bayyana aniyar rikidar da PDP zuwa ADC wannan batu yana nan kuma ana ci gaba da tattaunawa don kawo matsaya a siyasance.
Nan ba da jimawa ba za su tsayar da mikatin da za a dauka don rikidewa cikin wata jamiyyar saboda a ci gaba da shirin fito da Yan takarar da za fafata da su kafin zabukan 2027.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000