Shahararen Malamin Addinin Musulinci Dokta Idris Dutsen Tanshi Ya Rasu

Daga : Safiyanu Haruna Kutama

Fitaccen malamin addinin Islama da ke Jihar Bauchi, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya riga mu gidan Gaskiya.

Makusantan malamin sun tabbatar da rasuwarsa , Inda ya shafe tsawon lokaci Yana karantarwa da kuma harkar kasuwanci.

Malamin ya yi fama da rashin lafiya inda gabanin watan Ramadana ya fita neman magani a ƙasashen Masar da Saudiyya.

Za a yi jana’izarsa da ƙarfe 10 na safiyar Jumu’a a Masallacin Idi na Games Village da ke Jihar Bauchi.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane,sannan an kwato Drone.

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere