Babban Labari

ADC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamnanta a jihohi 28

Jam’iyyar ADC ta fitar da sunayen ’yan takararta na gwamna da mataimakin gwamna a jihohi 28 domin tunkarar zaɓen 2027. Jerin ya ƙunshi wasu fitattun ’yan siyasa, ciki har da tsohon ɗan takarar gwamnan Kaduna na PDP, Isa Ashiru, tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami. Sauran sun haɗa da tsohon ɗan takarar gwamnan Delta, Great Ogboru, […]

Read more

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

Allah Ya yi wa Mai martaba Sarkin Gumel, Alhaji Dakta Ahmed Muhammad Sani II, CON, rasuwa. Rasuwar Sarkin ta jefa al’ummar Masarautar Gumel da sauran al’ummar Jihar Jigawa cikin jimami da alhini, musamman kasancewarsa ɗaya daga cikin manyan sarakunan gargajiya da suka daɗe suna taka muhimmiyar rawa wajen jagoranci da zaman lafiyar al’umma. Sarkin ya […]

Read more

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.

Rundunar ƴansandan Jihar Kano ta sanar da daukar tsauraran matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya yayin bikin Takutaha na shekarar 2026, wanda za a gudanar a ranar Talata, 1 ga Satumba. Kwamishinan ’yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa al’ummar jihar bisa yadda suke gudanar da bikin cikin lumana, hadin kai da […]

Read more

Tinubu ya tafi hutun mako uku

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai yi bankwana da Abuja domin tafiya ƙetare hutun makonni uku a matsayin wani ɓangare na hutunsa na shekara-shekara. Sanarwar da Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce birnin Landan na ƙasar Birtaniya ne zai kasance wuri na […]

Read more