Home » Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Gobarar Kasuwar Farm Centre

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Gobarar Kasuwar Farm Centre

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani kwamitin bincike na musamman da zai duba gobarar da ta tashi a kasuwar wayoyin salula ta GSM da ke Farm Centre, a birnin Kano.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya jagoranci kaddamarwar a madadin Gwamnan Kano, inda ya ce kwamitin zai binciki musabbabin gobarar da kuma yadda za a hana faruwar irin ta nan gaba.

Ya ce an nada kwamitin ne domin ya gano ainihin dalilan gobarar, ya tantance irin barnar da aka yi, da kuma bayar da shawarwari masu amfani da za su hana sake faruwar irin hakan.

Ya kuma ja kunnen ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su guji siyasantar da batun tallafi ga wadanda gobarar ta shafa.

Ya ce dukkan gudummawa da tallafi ga ‘yan kasuwar da abin ya shafa za a rika karbarsu ta hannun kwamitin ko kuma ta asusun bankin da gwamnati ta ware domin hakan kamar yanda sanarwar Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Ciki Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar

Shugaban Kwamitin shi ne Kwamishinan Aiyuka na  Musamman na Jihar Kano, Alhaji Nasiru Sule Garo, kuma kwamitin ya kunshi wakilai daga hukumomin gwamnati, na tsaro, kungiyoyin ‘yan kasuwa, da masu zaman kansu.

Wasu daga cikin hukumomin da ke cikin kwamitin sun hada da Ma’aikatar Tsaro da Ayyuka na Musamman, Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Ciki, SEMA, Rundunar ‘Yan Sanda, DSS, KNUPDA, KACCIMA da kuma kungiyar ‘yan kasuwar GSM na Farm Centre.

Hukumomin tsaro a jihar Kano, sun kama wani mutum da ake zargi da yiwa matarsa kisan gilla ta hanyar yin amfani da Wuka ya daba mata a sassan jikinta.

Wasu shaidun gani da ido da suka bukaci asakaya sunansu, sun bayyana cewa wanda ake zargin, ya dade yana shan kayan maye, har sai da matarsa ta furta masa cewa idan bai daina ba, ba  zata sake barinsa ya kusance ta ba.

Rahotanni na cewa marigayiyar mai suna Maryam, wadda amarya ce, sai ba a bayyana sunan mijin nata ba.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata, lokacin da ake zargin mutumin ya sha kayan maye, inda ya bukaci matar tasa amma taki amincewa dashi, inda ya yi amfani da wuka wajen halaka ta.

Faruwar wannan lamari ya tayar da hankulan al’umar yankin kasancewar sunce basu saba ganin hakan ba.

Tuni jami’an yan sandan karamar hukumar Gwarzo suka samu nasarar kama wanda ake zargin, yayin da suka dauke gawar marigayiyar don gudanar da bincike.

Kawo yanzu rundunar yan sandan jihar Kano ba tace komai ba kan wannan lamari.

 

Sauran sun hada da wakilan kananan hukumomi, manyan jami’an gwamnati da masu bayar da shawara, inda Alhaji Abdulkadir Shehu AGS-HOC zai kasance Sakataren kwamitin.

AYYUKAN KWAMITIN SUN HADA DA:

 

  1. Binciken musabbabin gobarar.
  2. Kimanta barnar da ta auku da asarar rayuka idan akwai.
  3. Duba yadda hukumomi suka mayar da martani lokacin aukuwar gobarar.
  4. Tantance matakan kariya da ke kasuwar a halin yanzu.
  5. Bayar da shawarwari don hana aukuwar gobara a gaba.
  6. Tattaunawa da wadanda abin ya shafa da sauran shaidu.
  7. Tattara sunaye da bayanan wadanda suka yi asara.
  8. Nazarin tsarin gine-ginen kasuwar da tsaron muhalli.
  9. Samar da shawarwari kan yadda za a tafiyar da kasuwar cikin tsari.
  10. Karbar duk wata gudummawa cikin sahihin asusun gwamnati.
  11. Mikawa gwamnati cikakken rahoto cikin mako guda daga ranar da aka kaddamar da kwamitin.

Gwamnatin Kano ta ce tana daukar wannan lamarin da matukar muhimmanci kuma tana da niyyar sake gina kasuwar cikin tsari da kariya daga afkuwar gobara a gaba.

Ta kuma bukaci hadin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar aikin kwamitin da kuma rage radadin da gobarar ta haifar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?