Hukumomin tsaro a jihar Kano, sun kama wani mutum da ake zargi da yiwa matarsa kisan gilla ta hanyar yin amfani da Wuka ya daba mata a sassan jikinta.
Wasu shaidun gani da ido da suka bukaci asakaya sunansu, sun bayyana cewa wanda ake zargin, ya dade yana shan kayan maye, har sai da matarsa ta furta masa cewa idan bai daina ba, ba zata sake barinsa ya kusance ta ba.
Rahotanni na cewa marigayiyar mai suna Maryam, wadda amarya ce, sai ba a bayyana sunan mijin nata ba.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata, lokacin da ake zargin mutumin ya sha kayan maye, inda ya bukaci matar tasa amma taki amincewa dashi, inda ya yi amfani da wuka wajen halaka ta.
- Yadda Za A Magance Matsalar Ƙwacen Waya- CP Wakili (Singham)
- Hukumar Tace Fina-Finai Ta Yabawa Dakunan Taro tare da Gidajen Wasanni Bisa Bin Doka Da Oda A Kano
Faruwar wannan lamari ya tayar da hankulan al’umar yankin kasancewar sunce basu saba ganin hakan ba.
Tuni jami’an yan sandan karamar hukumar Gwarzo suka samu nasarar kama wanda ake zargin, yayin da suka dauke gawar marigayiyar don gudanar da bincike.
Kawo yanzu rundunar yan sandan jihar Kano ba tace komai ba kan wannan lamari.
