Tsohon Gwamnan Jihar Abiya, kuma Sanata mai wakiltar Abiya ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ya bayyana hakan a shirin siyasa na gidan talabijin na Channel a daren ranar Lraba.
Kalu, ya ce babu wanda zai iya kayar da Tinubu a tsakanin Goodluck Jonathan, Atiku Abubakar, ko kuma Peter Obi.
Kalu, wanda ke ɗan jam’iyyar APC, ya ce gwamnatin Tinubu ta samu nasarori wajen farfaɗo da tattalin arziƙi.
A cewarsa, irin tagomashin da Tinubu ya shimfiɗa zai sa ’yan Najeriya su sake zaɓarsa a karo na biyu.
A gefe guda Kalu ya gargaɗi tsohon Shugaban ƘasaJonathan da kada ya tsaya takara, inda ya ce dokar ƙasa ta hana shi sake tsayawa takara.
Jonathan, ya shugabanci Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015, bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua.
- DSS Ta Saki Mahajjata 7 Da Ta Kama Da Zargin Ta’addanci
- Kamfanin Dala Inland Dry Port Ya Karyata Rahotannin DaKe Danganta Iyalan Ganduje Da Mallakar Wani Sashi Na Kamfanin
Wasu masana doka suna cewa kundin tsarin mulki bai ba shi damar sake tsayawa takara ba.
Kalaman Kalu na zuwa ne daidai lokacin da harkokin siyasar Najeriya suke ƙara ɗaukar zafi yayin da ake shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Jam’iyyar APC mai mulki tana ƙoƙarin kare matsayinta, yayin da jam’iyyun adawa irin su PDP da LP da jam’iyyar haɗaka ADC ke ƙoƙarin farfaɗowa bayan shan kaye a zaɓen 2023.
A zaɓen 2023, Tinubu ya lashe shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar APC, inda ya doke Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP.
Dukkaninsu sun soki sakamakon zaɓen ta hanyar kai ƙara kotu, amma Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Tinubu.