Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta sanar da cewa dukkanin maniyyatan jihar za su rika samun abinci sau uku a kullum yayin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
Babban Daraktan hukumar, Alhaji Ahmad Umar Labbo, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa, inda ya ce wannan tsari na daga cikin matakan da gwamnati ta dauka domin inganta jin daɗi da walwalar alhazai a ƙasar Saudiyya.
Ya ce shirin samar da abincin, wanda Gwamna Malam Umar Namadi ke ɗaukar nauyinsa, zai shafi dukkanin maniyyatan jihar, har da masu buƙatu na musamman ta fuskar abinci.
Labbo ya ƙara da cewa wannan mataki ya sanya Jigawa zama ɗaya daga cikin jihohin da ke kan gaba wajen kula da jin daɗin alhazai, yana mai jaddada cewa hakan na nuna ƙudurin gwamnati na tabbatar da gudanar da Hajji cikin nasara da kwanciyar hankali.
A cewarsa, hukumar ta tanadi dukkanin shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da cewa an aiwatar da shirin cikin nasara, tare da jaddada aniyar su na ci gaba da samar da ingantattun ayyuka ga alhazai.
Hukumar ta kuma, ta bakin Jami’in Hulɗa da Jama’a, Habibu Yusuf Babura, ta miƙa godiya ga Gwamna Namadi bisa goyon baya da kulawar da yake bai wa maniyyatan jihar.
Wannan na daga cikin shirye-shiryen da gwamnatin jihar ke yi domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin 2026.