Babban Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS), Muhammad Babandede, OFR, OCM (Spain), CGI (Rtd.), ya taya Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, GCON, murnar sake zama abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Babandede, wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu neman takarar Sanatan Jigawa ta Arewa maso Gabas a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka kammala kwanan nan, ya bayyana cewa sake tsayar da Shettima alama ce ta amincewa da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen tafiyar da harkokin gwamnati.
Ya ce, ci gaba da haɗin gwiwar Shugaba Tinubu da Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa na da muhimmanci wajen tunkarar ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, musamman ta fuskar tattalin arziki da tsaro, tare da ci gaba da ƙoƙarin bunƙasa ƙasa.
Babandede ya yi addu’ar Allah Ya ba Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima lafiya, hikima da kariya, domin ci gaba da gudanar da ayyukansu na hidimtawa Najeriya.
A cikin saƙonsa, ya ce:
“Ina taya Mai Girma Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, murnar sake tsayar da shi a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ina roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya ba ku hikima, ƙarfi da lafiya domin ci gaba da jagorantar ƙasa tare da fuskantar ƙalubalen da ke gabanta da kuma tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.”