Hukumar Alhazai ta ƙasa, NAHCON, ta sanar da cewa za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa ƙasa mai tsark daga ranar 3 ga Mayu. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara, ta fitar a wannan Talatar. A cewarta, jirgi na farko Kamfanin Flynas zai tashi daga Filin […]

Hukumar Alhazai ta ƙasa, NAHCON, ta sanar da cewa za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa ƙasa mai tsark daga ranar 3 ga Mayu.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara, ta fitar a wannan Talatar.

A cewarta, jirgi na farko Kamfanin Flynas zai tashi daga Filin Jirgin Sama na Gateway da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Ta ƙara da cewa wasu jirage za su tashi a rana guda, ciki har da Umza Air da Max Air daga Abuja, yayin da Air Peace zai tashi daga Legas, sannan wani jirgin na Kamfanin Flynas zai tashi daga Birnin Kebbi.

Hukumar ta ce ma’aikatanta, ciki har da tawagar likitoci, sun riga sun tafi domin shirye-shiryen tarbar alhazai a ƙasar Saudiyya.

NAHCON ta shawarci alhazai da su kiyaye jadawalin jirginsu, domin kowanne kamfani zai ɗauki fasinjojin da aka tsara masa ɗaya bayan ɗaya, kuma ba zai koma duk inda ya kammala ɗaukar maniyyatan ba kamar yadda aka tsara.

Haka kuma, an buƙaci kowane maniyyaci ya tabbatar yana cikin rukuni na mutane 45, tare da sanin jagororinsu da jami’an jiharsu kafin tafiya.

Shugaban hukumar, Ismail Abba Yusuf, ya tabbatar da cewa an kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin ganin an gudanar da Hajjin 2026 cikin nasara.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai