JIBWIS Gwallaga Sun Ziyarci A Sansanin Alhazai Na Jihar Bauchi Domin Bada Agaji

JIBWIS Gwallaga Suna Taimakawa A Sansanin Alhazai Na Jihar Bauchi

Daga Muazu Hardawa da Abdurrazak Musa Hamza Bauchi

Tawagar ‘Yan agajin JIBWIS na kungiyar Izalatil bidah waikamatis sunnah karkashin jagorancin Daraktan Agaji na Jihar Bauchi, Alhaji Umar Jabir, tare da Camp Commander, Alh Ahmad M. Fanta, sun ziyarci Sansanin Alhazai na Jihar Bauchi domin duba yadda Alhazan jihar suka fara sauka bayan fara dawowar su daga Kasa Mai Tsarki aikin hajjin 2026.

Tawagar da ta raka su ta haɗa da Sakataren Agaji, Amb. Ali Magaji, SSA Special Duties, Abdulmalik Abubakar Aliyu, SSA Media, Abdulrazak Musa Hamza, da sauran jami’ai.

A yayin ziyarar, tawagar ta duba yadda ake gudanar da harkokin karɓar Alhazai tare da tabbatar da cewa an samar da dukkanin abubuwan da suka dace domin walwala da jin daɗin maniyyatan da suka dawo daga aikin Hajji.

Da yake jawabi ga jami’an da ke gudanar da wannan aiki, Daraktan Agaji, Alh Umar Jabir, ya ja hankalin su da su kasance jakadu na gari, masu nuna nagarta, haƙuri, gaskiya da jajircewa wajen yi wa Alhazai hidima. Don haka Ya jaddada cewa kyakkyawar mu’amala da sadaukar da kai wajen gudanar da aiki na daga cikin abubuwan da ke ƙara ɗaukaka martabar jihar Bauchi da kuma tabbatar da nasarar wannan gagarumin aikin taimako.

Don haka ya yi adduah Allah Ya karɓi Hajjin Alhazan mu da suka gudanar, Ya kammala dawo da su gida lafiya cikin aminci da albarka.

Post masu alaƙa

AIG Garba Ahmed ya bukaci daliban Sakandaren ’Yan Sanda Dawakin Kudu su zama jakadu na gari.

Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu sha da dillancin miyagun ƙwayoyi a Kano – Anti-Phone Snatching Force.

Kwamitin yaki da shaye-shaye da fadan daba na Kano ya nemi hadin kan hukumomin tsaro