Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta kama wata mata mai shekaru 18, Fatima Dalha, bisa zargin caka wa mijinta mai shekaru 30 wuƙa a ciki, sakamakon saɓani da suka samu a kan waya, kuɗi da turamen atamfa.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6 na safiyar ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, 2026, a ƙauyen Lirr Bajar da ke Ƙaramar Hukumar Dass ta jihar.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Nafi’u Habib ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a Bauchi.
Ya ce matar ta samu saɓani da mijinta ne yayin da ta ke neman ya ba ta kuɗinta, atamfarta da wayarta, waɗanda ta ce suna hannunsa.
Ya ce saɓanin ya ƙara tsananta har ya rikide zuwa faɗa, inda ake zargin matar ta ɗauki wuƙa ta caka wa mijin a ciki.
A cewar kakakin, mijin ya faɗi yana zubar da jini, lamarin da ya fusata jama’a suka taru tare da ƙoƙarin kai wa matar hari.
Sai dai jami’an ’yan sanda da suka isa wajen cikin gaggawa sun kuɓutar da matar daga hannun jama’a, yayin da aka garzaya da mijin asibiti.
Har yanzu yana kwance a asibiti inda likitoci ke kula da shi.
Nafi’u, ya ce an kama matar, kuma an gano wuƙar da ake zargin ta yi amfani da ita.
Ya ƙara da cewa za a miƙa lamarin ga sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) da ke Bauchi domin gudanar da cikakken bincike.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi kira ga jama’a da su riƙa warware saɓanin da ke tsakaninsu cikin lumana.
Ya kuma gargaɗi jama’a da ka da su ɗauki doka a hannunsu, inda ya bayyana cewa rundunar za ta tabbatar da adalci yayin gudanar da bincike a kan lamarin.