Farashin kayayyakin masarufi sun karu a watan Yuli a Najeriya, duk da matakan da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka domin bunƙasa samar da kayayyaki a cikin gida, da nufi sanar da sauƙi ga ’yan ƙasa rage kashe kuɗin sarrafa kayayyaki.
Hauhawwar farashin ya haifar da damuwa game da tasirin matakan da gwamnatin ƙasar take ɗauka domin samar da sauƙin farashin kayan abinci.
Sabbin alƙaluman da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar sun nuna farashin kayan abinci ya ƙaru da kashi 20.31 cikin 100 a cikin watanni 12 da suka gabata.
Rahoton ya nuna cewa farashin kayayyaki na ci gaba da hauhawa a cikin watan Yuli, duk kuwa da raguwa alƙaluman hauhawwar farashin na shekara-shekara idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Jerin jihohin da farashin ya fi hauhawwa ita ce, Adamawa “Adamawa (17.02%), Legas (13.48%). Duk da haka, an samu saukar farashi a Borno (13.26%), Jigawa (-3.68%), Kebbi (-3.67%), da kuma Bauchi (-1.85%), ” a cewar rahoton.
Iyalai da dama dai ba su shaida tasirin matakan da gwamnati ta ɗauka ba wajen rage musu tsadar kayayyakin abinci.
Alƙaluma na wata-wata da NBS ta fitar sun nuna an kayayyakin abinci da ake yawan amfani da su sun tashi, kamar shinkafa, dawa, doya, albasa, fulawa, tumatir, garin kwaki da sauransu.
Yanayin alkaluman ya nuna farashin kayayyanki sun karu daga watan Yuni zuwa Yuli duk da cewa yanayin tashin bai kasance da sauri ba kamar yadda aka samu a watan baya na Yun
