• Home  
  • Rundunar yan sanda ta dawo da zaman lafiya a Bichi bayan rikicin magoya bayan APC da NDC a Kano.
- Labarai

Rundunar yan sanda ta dawo da zaman lafiya a Bichi bayan rikicin magoya bayan APC da NDC a Kano.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama mutane takwas da ake zargi da hannu a wani rikicin siyasa da ya ɓarke tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da NDC a garin Bichi dake jihar. Rikicin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 4:45 na yammacin Lahadi, 15 ga Nuwamba, 2026, ya yi sanadiyar lalata motoci 13 da […]

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama mutane takwas da ake zargi da hannu a wani rikicin siyasa da ya ɓarke tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da NDC a garin Bichi dake jihar.

Rikicin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 4:45 na yammacin Lahadi, 15 ga Nuwamba, 2026, ya yi sanadiyar lalata motoci 13 da wasu kayayyakin yaƙin neman zaɓe, ciki har da fastoci da allunan talla.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya ce mutane biyar sun samu raunuka sakamakon rikicin, kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.

Sanarwar ta bayyana cewa jami’an ’yan sanda sun gaggauta isa wurin bayan samun rahoton rikicin, inda suka yi nasarar shawo kan lamarin tare da dawo da zaman lafiya.

Haka kuma, rundunar ta ce ta ƙwato wasu abubuwa da suka haɗa da gariyo guda ɗaya, adduna biyu, sanduna, kwalbar wani sinadari guda ɗaya da kuma  “Suck and Die” a yankin.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi Allah-wadai da rikicin, yana mai gargaɗin cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na tayar da tarzoma ko kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma ba kafin zaɓe da lokacin zaɓe da ma bayan zaɓen.

Ya kuma jaddada cewa dole ne dukkan harkokin siyasa su gudana cikin lumana da bin doka, yana mai cewa babu wani mutum ko wata ƙungiya da ta fi ƙarfin doka.

A cewar sanarwar, an kai waɗanda ake zargin zuwa Sashen binciken manyan laifuka na jihar Kano (SCID), da ke Bompai, domin gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala binciken.

Rundunar ta yi kira ga shugabannin siyasa da magoya bayan jam’iyyu da su guji tashin hankali, tare da bin doka da oda, sannan ta buƙaci jama’a da su kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai