Dakarun Operation Fansan Yamma sun daƙile hare-haren ’yan ta’adda da suka kai wasu yankuna biyu a Ƙaramar Hukumar Anka ta Jihar Zamfara, tare da hallaka da dama daga cikin maharan.
Hare-haren sun faru ne a ranar 14 ga watan Nuwamba a ƙauyukan Wuya da Yarzabia.
A cewar rundunar sojin, ’yan ta’addan sun isa yankunan ne a kan babura, amma sojoji sun fafata da su tare da tilasta musu ja da baya.
Daga baya, maharan sun sake haɗuwa tare da kai wani sabon hari, amma sojojin sun sake fatattakar su.
Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta tura jirgin yaƙi domin tallafa wa dakarun sojin ƙasa.
Jirgin ya gano wasu ’yan ta’adda na ƙoƙarin kwashe garken shanun da ake zargin na sata ne, inda ya yi musu ɓarin wuta ta sama tare da hallaka da yawa daga cikinsu.
A wani samame na daban aka kai Jihar Kaduna, wanda sojoji sun kashe wani da ake zargin ɗan ta’adda ne yayin musayar wuta a ƙauyen Aguba da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru.
Sojojin sun kuma ƙwato bindigogi ƙirar gida guda biyu, wayar hannu da wasu ƙwayoyi.
A wani artabu kuma da ya gudana a kan hanyar Buruku zuwa Kaduna, wasu ’yan ta’adda sun tsere zuwa cikin daji, inda suka bar babura guda biyu a hannun sojoji.
Rundunar sojin ta ce dakarunta na ci gaba da gudanar da samame domin hana ’yan ta’addan sake haɗuwa da kai wasu hare-haren.
Ta yaba wa sojojin bisa ƙoƙarinsu, tare da kira ga al’umma da su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.
