• Home  
  • Ambaliya Ta Karya Gada A Kasar Nijar
- Babban Labari - Labarai

Ambaliya Ta Karya Gada A Kasar Nijar

Daga Suraj Na Iya Idris Kududdufawa Babbar gadar da ake shiga babban birnin Yamai a kasar Nijar ta karye sakamakon mamakon ruwa saman da ake yi samu a yankin.  Gadar ta karye ne tsakanin mahadar jihar Doso da mahadar shiga birnin na Yamai. Mafiya yawan al’ummar da suke bi ta jihar Doso domin shiga birnin […]

Daga Suraj Na Iya Idris Kududdufawa

Babbar gadar da ake shiga babban birnin Yamai a kasar Nijar ta karye sakamakon mamakon ruwa saman da ake yi samu a yankin. 

Gadar ta karye ne tsakanin mahadar jihar Doso da mahadar shiga birnin na Yamai.

Mafiya yawan al’ummar da suke bi ta jihar Doso domin shiga birnin sun hakura da shiga.

A yanzu dai haka akwai motocin matafiya a jibge a hanyar sakamakon wannan lamari da ya afku na karyewar gadar.

Akwai mutane daga jihoshi da dama a kasar Niger da sai sun bi ta jihar Doso sannan su isa birnin suma lamarin ya ritsa dasu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai