Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya buƙaci Gwamnatin Najeriya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa manufofin tattalin arziƙin ƙasar sun kare muradun mutane masu ƙaramin ƙarfi.
Daraktar Hulɗa da Jama’a na IMF Julie Kozack ce ta bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a Washington, D.C babban birnin Amurka.
- Yan Bindiga Sun Saki Birgediya Janar Tsiga
- Kisan Gillar Uromi : Gwamnatin Kano Ta Yaba Wa Shugaba Tinubu Da Gwamnan Edo
Julie ta jaddada muhimmancin bai wa talakawan Najeriya masu fama da ƙuncin rayuwa tallafin kuɗi sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙin da gwamnatin shugaba Tinubu ta bijioro da su.

