• Home  
  • Kisan Gillar Uromi : Gwamnatin Kano Ta Yaba Wa Shugaba Tinubu Da Gwamnan Edo
- Babban Labari

Kisan Gillar Uromi : Gwamnatin Kano Ta Yaba Wa Shugaba Tinubu Da Gwamnan Edo

  Daga: Hassan Abdu Mai Bulawus Gwamnatin Jihar Kano ta gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, saboda gaggawar ɗaukar matakin da suka yi bayan kisan gillar mutane 16 ’yan asalin Kano a Udene, da ke ƙaramar hukumar Uromi ta Jihar Edo. Gwamna Abba Kabir Yusuf, a cikin wata […]

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce sun yi nasarar kwato filayenta na triliyoyin Nairori

 

Daga: Hassan Abdu Mai Bulawus

Gwamnatin Jihar Kano ta gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, saboda gaggawar ɗaukar matakin da suka yi bayan kisan gillar mutane 16 ’yan asalin Kano a Udene, da ke ƙaramar hukumar Uromi ta Jihar Edo.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa-hannun Kwamishinan Yaɗa Labarai, Kwamared Ibrahim Waiya, ya yaba wa tawagar Gwamnatin Tarayya da Gwamnan Edo saboda ta’aziyyar da ya zo Kano, da kuma kudurin su na tabbatar da adalci ga waɗanda aka kashe.

Gwamnan ya sake buƙatar a gudanar da shari’a ta gaskiya, tare da bayyana waɗanda aka kama a fili, domin tabbatar da cewa an yi adalci.

Ya kuma yaba wa Gwamnan Edo saboda tattaunawa da al’ummar Hausawa a Jihar Edo da kuma alƙawarin biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu.

Haka kuma Gwamnan ya yaba Shugaba Tinubu bisa umarnin da ya bai wa hukumomin tsaro domin gano waɗanda ke da hannu a kisan, wanda ya bayyana hakan a matsayin ƙwazon da Gwamnatin Tarayya ta nuna wajen kare dukkan ’yan Najeriya.

Gwamnatin Jihar Kano ta kuma yi alƙawarin ci gaba da sa ido kan lamarin don tabbatar da adalci da biyan diyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai