• Home  
  • Gobe Za A Rufe Kasuwar Singa Domin Yashe Magudanan Ruwa
- Babban Labari - Kasuwanci - Labarai

Gobe Za A Rufe Kasuwar Singa Domin Yashe Magudanan Ruwa

Hukumar kasuwar Singa da ke Kano ta ce za gobe Lahadi ga Yuni, 2025, ba za a gudanar da harkokin kasuwanci ba daga ƙarfe 7 na safe zuwa 7 domin aikin yashe magudanan ruwa.

Hukumar kasuwar Singa da ke Kano ta ce gobe Lahadi 15 ga Yuni, 2025, ba za a gudanar da harkokin kasuwanci ba daga ƙarfe 7 na safe zuwa 7 domin aikin yashe magudanan ruwa.

Wannan na cikin wata sanarwa da shugaban Hukumar Gudanarwar Kasuwar Singa, Barr. Junaidu Muhammad Zakari, ya fitar.

Ya ce aikin na ranar Lahadi zai kasance aikin gayya na musamman da ya haɗa dukkanin masu ruwa da tsaki a kasuwar, tare da nufin tsaftace muhalli da inganta yanayin kasuwanci, musamman a lokacin damina ke kankama.

Shugaban hukumar ya buƙaci ’yan kasuwa da maziyartan kasuwar da su ba da haɗin kai tare da bin umarnin rufewar domin gudanar da aikin cikin tsari da kwanciyar hankali.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai