• Home  
  • An Kai Matashin Da Ya Yi Yunkurin Fadowa Daga Allon Talla Asibitin Yan Sandan Kano.
- Babban Labari - Labarai

An Kai Matashin Da Ya Yi Yunkurin Fadowa Daga Allon Talla Asibitin Yan Sandan Kano.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ceto wani matashi mai suna Ibrahim Abubakar, mai shekaru 19 da yayi yunkurin kashe kansa ta hanyar fadowa daga kan allon talla (billboard) akan gadar Ado Bayero kusa da kan titin zuwa Maiduguri Road a jihar. Mukaddashin kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, DSP Hussaini Abdullahi, ne ya bayyana […]

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ceto wani matashi mai suna Ibrahim Abubakar, mai shekaru 19 da yayi yunkurin kashe kansa ta hanyar fadowa daga kan allon talla (billboard) akan gadar Ado Bayero kusa da kan titin zuwa Maiduguri Road a jihar.

Mukaddashin kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, DSP Hussaini Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aike wa da manema labarai.

Rahotanni na cewa matashin yayi barazanar fadowa kasa matukar wani dan Tiktok mai suna Abdul BK bai zo ba.

DSP Hussaini, ya ce bayan samun rahotan kwamishinan yan sandan jihar , ya tura tawagar jami’an tsaro tare da hadin gwiwar ma’aikatan hukumar kashe gobara ta jihar Kano, inda suka ziyarci wajen da gaggawa har aka ceto shi.

Sanarwar ta kara da cewa sakamakon, a wannin da matashin ya shafe a saman allon , ya wahala sosai saboda yunwar da yake ji, kuma bayan sauko dashi an garzaya dashi asibitin yan sanda dake unguwar Bompai don samun kulawar gaggawa.

Bayan sakko dashi, Abdul Bk, ya bayyana bacin ransa kan yadda matashin ya so halaka kansa , inda ya shawarci matasa da su dena jefa kansu cikin hadari.

Ya ce lokacin da aka fada masa yana bacci, inda ya harzanta ya toho domin ceto rayuwarsa.

 

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori , ya yabawa jami’an tsaron bisa hanzartawa da suka yi wajen ceto rayuwar matashin, inda ya tabbatar da cewa rundunar zata ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

CP Bakori, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan faruwar lamarin , kuma ya gargadi jama’a da su guji irin wannan danyen aiki domin duk wanda kaa samu za a hukunta shi.

A karshe rundunar ta shawarci dukkan wadanda suke fama da wata matsala ta rayuwa da su nemi taimako, a inda ya dace.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai