Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi nasarar shawo kan rikicin da ya kunno kai tsakanin Matatar Man Ɗangote da Ƙungiyar Ma’aikatan Dakon Man Fetur da Gas (NUPENG).
Bayan zaman da aka gudanar a babban ofishin DSS da ke Abuja, shugabannin NUPENG suka bayar da umarnin a dakatar da yajin aikin da aka fara a faɗin ƙasar.
Zaman ya samu halartar Ministan Kuɗi, Wale Edun; Ministan Kwadago, Mohammed Maigari Dingyadi; da Ƙaramin Ministan Kwadago, Nkeiruka Onyejeocha. Haka nan, tawagar kamfanin Ɗangote ƙarƙashin jagorancin Alhaji Sayyu Dantata ta halarci taron tare da shugabannin ƙwadago daga NUPENG, NLC da TUC.
A baya, taron da aka yi ranar Litinin bai haifar da da mai ido ba, inda NUPENG ta nuna adawa da matakin Matatar Ɗangote na fara jigilar mai zuwa gidajen mai kai tsaye.
- Yan Sanda Sun Kama Mutanen Da Ake Zargi Da Lalata Taransifoma A Hadejia
- Kungiyar Lauyoyi Ta Bukaci Mambobinta Su Yi Taka Tsan-tsan Wajen Yin Amafani Da Fasahar AI
Ƙungiyar ta ce matakin da Ɗangote ya ɗauka zai raba dubban ma’aikata da direbobin manyan motoci sama da 30,000 da aikinsu.
Sai dai yayin da ƙungiyar NOGASA ta nuna goyon baya ga NUPENG, ƙungiyar AROGMA ta Arewacin Najeriya ta yi maraba da matakin Ɗangote.

