Wani mamakon ruwan sama da aka tafka a birnin Zariyan jihar Kaduna, ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku yayin da kuma ake ci gaba da neman gawar mutum daya.
Bayanai sun nuna cewa biyu daga cikin wadanda suka rasa ransu dalibai ne, Fatima Sani Danmarke mai shekara 18, da ke karatu a makarantar share fagen shiga jami’a da ke Funtua a jihar Katsina da Yusuf Surajo da shi kuma yake karatu a Zariya, sai kuma yarinyar da Fatima ke goye da ita.
Wani da lamarin ya faru a gabansa, Mallam Mustapha Badamasi Danbakano, ya ce, “Bayan ruwa ya ɗan yi sauƙi sai muka hangi wani mai babur mai kafa uku yana kokarin sauke wata yarinya goye da wata karamar yarinya a bayanta.
“To sakamakon ruwan saman da ya rufe ko ina ba a iya gane a inda kwalbati yake, ita kuma tana ja da baya don neman inda za ta tsallaka kawai sai ta faɗa cikin kwalbatin ita da goyon da take dauke da shi.
“Shi ma kuma mai babur din sai ya shiga ciki domin ya ceto su, nan take ruwan ya wuce da su gaba daya,” in ji shi.
- DSS Ta Shawo Kan Rikicin NUPENG da Ɗangote
- Yan Sanda Sun Kama Mutanen Da Ake Zargi Da Lalata Taransifoma A Hadejia
Ya kara cewa daga nan ne sai wani dalibi mai suna Yusuf Surajo da ke gefe ya zaburo da gudu ya fada ruwan da nufin ya ceto su, shi ma haka ruwan ya tafi da shi.
Imam Mallam Musa Umar Almishawi Wanda ya jagoranci sallar jana’izar dalibin ya ce marigayin ya sami babban rauni a goshinshi sakamakon bugun da wani karfe da ya yi masa a cikin ruwan.
Ita kuwa daliba Fatima da goyon ta na ’yar shekara uku ba a riga anyi jana’izar su ba zuwa lokacin da ake hada wannan rahoton.
Aminiya ta gano cewar ya zuwa yanzu an gano gawarwakin mutane uku a daidai gadar makarantar firamare ta Isan Nabawa da ke unguwar Tudun Wada Zariya.
Sai dai har yanzu ana ci gaba da kokarin gano gawar matukin babur mai kafa ukun amma ba a kai ga gano shi ba.

