Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) ta kama jabun magungunan zazzaɓin cizon sauro da darajarsu ta kai sama da ₦1.2bn a Legas.
A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X ranar Juma’a, hukumar ta ce jami’anta sun kai samame a wani ɗakin ajiyar kaya da ke Ilasa-Oshodi, inda suka gano katan 277 na maganin Malamal Forte na bogi.
NAFDAC ta bayyana cewa an ɓoye magungunan cikin kwalayen da aka yi wa lakabi da Diclofenac Potassium 50mg, waɗanda aka shigo da su ba bisa ƙa’ida ba daga Shanɗi Tianyuan Pharmaceuticals Group da ke ƙasar China.
- Gwamnan Kano Ya Aike Wa Majalisa Dokar Haramta Auren Jinsi.
- Yan Najeriya Sun Kusa Fara Shan Wutar Sa’o’i 24 — Minista
Darakta-Janar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce wannan na daga cikin matakan hukumar wajen murƙushe masu safarar magungunan jabu.
“Wannan aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin kare lafiyar al’umma da tabbatar da cewa ’yan Najeriya na amfani da magunguna masu inganci kawai,” in ji ta.

