Fitacciyar mai girkin nan, Hilda Effiong Bassey, wadda aka fi sani da Hilda Baci, ta sake kafa tarihi a duniya ta hanyar girka tukunyar dafa-dukar shinkafa mafi girma bayan shafe awa takwas tana girkin.
Hakan dai na ƙunshe ne cikin wani saƙon taya murna da Kundin Bajinta na Guinness ya wallafa a shafukan sada zumunta.
Hilda Baci dai ta dafa shinkafa dafa-duka mafi yawa a tarihi tare da sauran kayan haɗi da sunadaran ɗanɗano wadda nauyinta ya kai kilo 8,780 a yankin Victoria Island da ke Legas.
A shekarar 2023 Hilda mai shekaru 28 ta shiga Kundin Bajinta na Guiness World Record bayan shafe awa 93 da mintuna 11 tana girke-girken abinci iri-iri.
A wannan karon, Hilda ta girka ƙananan buhuna 200 na shinkafa wanda nauyinsu ya kai kilo 4,000 da katan 500 na tumatir da kilo 600 na albasa da sauran kayan haɗi.
- Sifaniya Ta Buƙaci A Haramta Wa Isra’ila Shiga Gasar Wasannin Duniya
- An Tsinci Gawar Wani Barasaken Gargajiya A Filato
An gudanar da zaman girkin a fili a cikin birnin kasuwanci na Legas, lamarin da ya ja hankalin ɗaruruwan masu kallo.
Dafa-dukar shinkafa wadda a wasu harsunan ake kira Jollof rice abinci ne da ake sha’awa sosai a yankin Yammacin Afirka, inda ƙasashe kamar Nijeriya, Ghana, Senegal, Kamaru, da Gambiya ke da’awar cewa su ne ke da mafi ƙwarewa a wurin girka ta.
A shekarar 2023, Hukumar Ilimi, Kimiyya, da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta amince da Senegal a matsayin wurin da wannan abinci na dafa-dukar shinkafa ta samo asali.

