• Home  
  • Za A Rataye Sojan Najeriya Saboda Halaka Ɗan Keke Napep
- Babban Labari - Labarai

Za A Rataye Sojan Najeriya Saboda Halaka Ɗan Keke Napep

Wata babbar kotun sojin Najeriya da ke zamanta a sansanin sojoji ta Maxwell Khobe da ke Jos, Jihar Filato ta yanke wa soja mai suna Lukman Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Wata babbar kotun sojin Najeriya da ke zamanta a sansanin sojoji ta Maxwell Khobe da ke Jos, Jihar Filato ta yanke wa soja mai suna Lukman Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An yanke masa hukuncin ne bayan an same shi da laifuka biyu: kisan gilla ga direban babur mai ƙafa uku, Abdulrahman Isa, a Azare (Bauchi), da kuma mallakar harsasai ba bisa ƙa’ida ba.

Shaidu sun tabbatar cewa Musa ya haɗa baki da wani mai suna Oba, suka kai Isa gidansa da sunan taimaka masa wajen kwashe kaya, daga nan Musa ya bugi Isa a kai da katako, ya suma, sannan ya shaƙe shi ya mutu.

Domin ɓoye laifin, suka saka gawar cikin buhu, suka jefa tsakanin ƙauyukan Shira da Yala (Bauchi). Babur ɗin da marigayin ke amfani da shi daga baya aka sayar da shi, wanda ya yi sanadiyyar fallasuwar lamarin.

A cikin shari’ar, an tabbatar da cewa Musa ya mallaki harsasai 34 ba tare da izini ba.

Da yake yanke hukunci, Birgediya Janar Liafis Bello ya bayyana kisan a matsayin abin kunya, rashin tausayi, cin zarafi, da kuma rashin ɗa’a da zubewar kimar sojoji. Bello ya ce Musa ya koma daga kare ’yan ƙasa zuwa mai kisan gilla, abin da ya zubar wa rundunar da mutunci.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai