Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yi afuwa ga Maryam Sanda, wadda aka yankewa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa samun ta da laifin halaka mijinta, mai suna Bilyaminu Bello.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar , inda ya ce matakin ya zo ne bisa shawarar kwamitin da ke duba batun yafewa ma su laifi a Najeriya.
- Gidauniyar SURE 4U Ta Tallafawa Iyayen Marayu 1689 A Hadejia Jihar Jigawa.
- Yan Sanda Sun Kubutar Mutane 3 Daga Hannun Masu Garkuwa A Jahohin Kano Da Kaduna
Maryam Sanda, mai shekaru 37 a duniya , ta shafe shekaru shida a gidan yarin Suleja kafin samun afuwa daga fadar shugaban kasar Nijeriya.

