• Home  
  • An Kama Wanda Ake Zargi Da Kunnawa Tsohuwar Budurwarsa Wuta A Oyo
- Babban Labari - Labarai

An Kama Wanda Ake Zargi Da Kunnawa Tsohuwar Budurwarsa Wuta A Oyo

Rundunar yan sandan jihar Oyo, ta kama wani matashi mai suna Lawan Faruq, bisa zarginsa da kunnawa tsohuwar budurwarsa wuta, bayan ta yanke alakar soyayyar dake tsakaninsu. Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X. Wanda ake zargin ya cinnawa tsohuwar budurwar tasa wuta a barikin sojoji dake […]

Rundunar yan sandan jihar Oyo, ta kama wani matashi mai suna Lawan Faruq, bisa zarginsa da kunnawa tsohuwar budurwarsa wuta, bayan ta yanke alakar soyayyar dake tsakaninsu.

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Wanda ake zargin ya cinnawa tsohuwar budurwar tasa wuta a barikin sojoji dake Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Rahotanni na cewa Lawal Faruq, ya dauki matakin kan zargin karya alkawari da masoyiyar tasa tayi na yanke alakar soyayyarsu, inda ya yi amfani da fetur ya zuba mata sannan ya kyasta ashana.

An garzaya da budurwar mai suna Omolola Hassan wani asibiti lokacin da jami’an sojoji suka kai mata daukin gaggawa.

 

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000