Hukumar wayar da kan jama’a ta Nijeriya NOA, ta sanar da sabbin ka’idojin yadda za a rera taken kasar a tarukan gwamnati.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da fitar, inda ta ce daga yanzu za a dinga rera baitin farkon ne kawai , a dukkan tarukan gwamnati mai makon baitoci uku da aka saba yi aba ya.
Sai dai sanarwar ta ce cikakken baitocin ukun na taken kasar za a dinga rera sune a lokuta na musamman, kamar ranar yan cin kai ta 1 ga watan Oktoba da kuma ranar rantsar da shugaban kasa da ranar tunawa da sojoji 15 ga watan janairun da kuma 12 ga watan Yuni wato ranar Demokuradiya.
- NOA Ta Bukaci Dalibai Su Ci Gaba Da Martaba Nijeriya Da Al’adunsu.
- Saudiyya Ta Rage Wa Najeriya Kujerun Aikin Hajjin 2026
Haka zalika za adinga rera taken Nijeriya cikakke a ranar rantsar da majalissun dokokin kasa da sauransu.
NOA ta ce ta dauki matakin ne don daidaita yadda ake rera taken kasa, da kuma farfado da al’adun kishin kasa tsakanin Yan Nijeriya musamman matasa, inda ta jadda cewa sabon tsarin zai taimaka wajen tabbatar da nustuwa ladabi da kuma girmamawa yayin rera taken kasar.
A watan mayun 2025 shugaban kasa Bola Ahmad Tonubu , ya sanya hannu kan kudirin dawo da tsohon taken Nijeriya.