• Home  
  • Tinubu Ya Cire Sunan Maryam Sanda Daga Waɗanda Ya Yi Wa Afuwa
- Babban Labari - Labarai

Tinubu Ya Cire Sunan Maryam Sanda Daga Waɗanda Ya Yi Wa Afuwa

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Sanda wadda ke zaman jiran hukuncin kisa bisa samun ta da laifin kashe maigidanta. Wannan na ɗauke a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Tinubu kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar. A farkon watan Oktoba nan ne dai shugaba Tinubu ya yi wa […]

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Sanda wadda ke zaman jiran hukuncin kisa bisa samun ta da laifin kashe maigidanta.

Wannan na ɗauke a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Tinubu kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.

A farkon watan Oktoba nan ne dai shugaba Tinubu ya yi wa wasu mutum 175 afuwa da suka haɗa da matattu da masu rai.

 

Sai dai kuma shugaban ya fuskanci suka daga ɓangarori da dama na ƙasar, wani abun da ake ganin shi ya sa gwamnatin ta fito ta ce za ta sake waiwayar jerin sunayen.

 

A jerin sunayen na farko da aka fitar, ya ƙunshi mutum 175 ciki har da Maryam Sanda wadda aka yi ta sa-in-sa dangane da yi mata afuwar.

 

To sai dai sabon jerin sunayen mutanen ya ƙunshi mutum 34 ne kawai, inda aka kasa su gida uku waɗanda aka yi wa afuwa da waɗanda mayar da hukuncin kisar da aka yi musu zuwa ɗaurin rai da rai da kuma waɗanda aka yi afuwa amma ba tare da yafe musu laifin nasu ba.

 

Su ne mutum 15 da aka yafewa laifin da suka yi sannan kuma aka wanke su daga laifin wanda hakan ke nufin ba za a taɓa alaƙanta su da laifin ba sannan idan akwai wasu haƙƙoƙinsu da aka hana su sakamakon aikata laifin to yanzu za a ba su haƙƙoƙin nasu.

 

Mrs Anastasia Daniel Nwaobia

Barrister Hussaini Alhaji Umar

Ayinla Saadu Alanamu

Hon Farouk Lawan

Herbert Macaulay

Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa

Ken Saro Wiwa

Saturday Dobee

Nordu Eawo

Daniel Gbooko

Paul Levera

Felix Nuale

Baribor Bera

Barinem Kiobel

John Kpuine

Daga hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai

Wannan jerin sunayen mutum huɗu ne waɗanda aka rage girman hukuncin da aka yanek musu sakamakon laifin da suka aikata, inda aka rage hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai.

 

Emmanuel Baba

Abubakar Usman

Khalifa Umar

Mohammed Umar

Waɗanda aka yafewa amma tabon zai bi su

Oroka Michael Chibueze

Adesanya Olufemi Paul

Daniel Bodunwa

Hamza Abubakar

Buhari Sani

Mohammed Musa

Maharazu Abubakar

Ibrahim Yusuf

Saad Ahmed Madaki

Kofur Michael Bawa

Richard Ayuba

Adam Abubakar

Emmanuel Yusuf

Chinedu Stanley

Johny Ntheru Udor.

Sanarwar da Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ta ce shugaba Tinubu ya sake waiwayar jerin sunayen mutanen da aka yi wa afuwar ne sakamakon tuntuɓar Majalsiar Ƙasa da kuma ra’ayoyin ƴan Najeriya kan batun.

“Shugaban ƙasa ya yi umarnin a sake bibiyar da waiwayen jerin sunayen waɗanda aka yi wa afuwar da farko…inda aka goge sunayen mutanen da suka aikata manyan laifuka kamar garkuwa da mutane da safarar ƙwaya da safarar bil’adama da damfara da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba….sannan kuma aka rage hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai ga wasu waɗanda aka yafewa a farko.”

Sanarwar ta ƙara da cewa ɗaukar matakin ya zama dole ne bisa la’akari da girman laifukan da alaƙarsu da matsalar tsaro da ƙasar ke ciki da kuma nuna damuwa da halin da ƴan uwa da iyalan wadanda masu laifin suka saɓawa

“Shi adalci abu ne mai fuska uku – Wanda ya aikata laifi da wanda aka yi wa laifin da kuma ƙasa ko kuma al’umma saboda haka ne ma aka yi wani waiwayen,” in ji sanarwar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai