Jagoran ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu ne da asubahin ranar Alhamis.
Malamin ya rasu ne a wani asibiti da ke jihar Bauchi.sakamakon ƴar gajeriyar jinya.
Majiyoyi daga iyalansa sun ce za a yi jana’izar shehin malamin ne a ranar Juma’ah.
Fitaccen malamin addinin Musuluncin ya rayu tsawon shekaru 100 a duniya, inda ya rasu ya bar ƴaƴa da jikoki masu yawa.

