Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin samar da jirage marasa matuƙa da sauran kayan aikin tsaro domin sa ido da kuma ɗaukar mataki cikin gaggawa don kare rayuka da dukiyoyin mazauna yankunan iyakar Kano da Katsina.
Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake ziyartar sansanonin rundunar hadin gwiwa (JTF) domin tantance yadda suka shirya daƙile hare-haren ‘yan bindiga da suka auku a kwanakin baya a ƙananan hukumomi guda uku na Tsanyawa da Shanono.
Ya kuma yi kira ga al’ummar da ke zaune a yankunan da abin ya shafa da su taimaka wa rundunar JTF da bayanai masu amfani game da motsin ‘yan bindiga.
Gwamnan ya ce yayin da ya kai ziyara ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu kan lamarin, shugaban ya amsa buƙatar da aka gabatar masa cikin sauri.”
Ya umarci JTF da su yi Iya kokarinsu wajen tabbatar da kuɓutar da mutanen da aka sace a kananan hukumomin Tsanyawa da Shanono daga hannun ‘yan bindigar.
- Yau Majalisar Dattawa za ta tantance sabon Ministan Tsaro
- Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi
“Mun san cewa suna kai hari kan al’umma ba gayra ba dalili, musamman a Tsanyawa da Shanono. Rayuka da dama sun salwanta, yayin da wasu kuma aka kai su daji. Insha Allah, za a dawo da wadanda aka sace ga iyalansu,” in ji shi.
Gwamna Yusuf ya kara da cewa, “Mun yi wannan ziyarar ne domin tantance halin tsaro da kuma tattauna da ku, haka zalika saboda ƙarfafa gwiwar ku wajen yin aiki tuƙuru.”
Ya bayyana damuwarsa cewa irin wannan rashin tsaro a Kano sabon lamari ne da ba a saba gani ba, amma gwamnatin jihar na yin duk mai yiwuwa tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro domin magance matsalar.
A yayin ziyarar, Gwamna Yusuf ya taya iyalan wadanda aka sace jimami tare da tabbatar masu cewa za a dawo da su cikin gaggawa.
An ruwaito cewa mutum 5 da 10 ne aka sace a Tsanyawa da Shanono, ciki har da mace daya da ta rasa rayuwarta sakamakon hare-haren.

