• Home  
  • Jihar Kano tana cike da masu yaɗa labaran ƙarya – CP Ibrahim Adamu Bakori.
- Babban Labari - Labarai

Jihar Kano tana cike da masu yaɗa labaran ƙarya – CP Ibrahim Adamu Bakori.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta ce ba zata ɗaga ƙafa ga masu yaɗa labaran ƙarya ko kalaman batancin da zai tayar da hankalin al’umma ba, musamman a shafukan sada zumunta da kafafen yada labarai. Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan, a wajen bitar wayar kai, don  yaƙi da […]

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta ce ba zata ɗaga ƙafa ga masu yaɗa labaran ƙarya ko kalaman batancin da zai tayar da hankalin al’umma ba, musamman a shafukan sada zumunta da kafafen yada labarai.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan, a wajen bitar wayar kai, don  yaƙi da labaran ƙarya da kalaman batanci a jihar.

Rundunar yan sandan jihar Kano ce, tare da haɗin gwiwar gidauniyar Aminu Garba Mashi da kungiyar YOSPIS, ne suka shirya taron don wayar da kan jama’a kan illar da yaɗa labaran ƙarya ko kalaman ɓatanci ke haifarwa ga al’umma.

CP Bakori, ya ƙara da cewa jihar Kano, tana cike da masu yaɗa labaran ƙarya, kuma ba za su bari a ci mutuncin mutane ba, don haka a matsayinsu na jami’an tsaro suke ɗaukar dukkan matakan hana tayar da hankali.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce labaran ƙarya da wasu ke yi laifi ne don haka ne suke ƙara sanar da al’umma domin ba za a ƙyale duk wanda aka samu da laifin ba.

Anata ɓangaren Daraktan kungiyar YOSPIS, Zainab Nasir Ahmad, ta bayyana cewa, ba wannan ne karon farko ba, na shirya irin wannan bitar, kuma zaɓe na kara ƙaratowa, inda ake samun wasu suna yin kalaman dake ƙara tunzura mutane.

Taron bitar ya samu halattar, baturen yan sandan jihar Kano da sauran hukumomin tsaro, da wakilan gwamnati da masu riƙe da sarautun gargajiya da kafafen yada labarai da kungiyoyi da ma’abota shafukan sada zumunta.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000