NECO ta saki sakamakon jarrabawar 2025 na dalibai masu zaman kansu

Hukumar Jarrabawa ta Kasa (NECO) ta saki sakamakon jarrabawar dalibai masu zaman kansu na shekarar 2025.

Shugaban Hukumar Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya bayyana cewa 93,425 daga cikin daliban sun zana jarrabawar harshen Ingilishi, inda kashi 78.32% (73,167) suka samu akalla Credit. Dalibai 93,330 sun zana jarrabawar Lissafi inda kashi 91.35 % (85,256) suka samu akalla Credit.

Ya bayyana cewa dalibai 95,160 ne suka zana jarrabawar daga cikin 96,979 da suka yi rajistar jarabwar, maza 51,823 da mata 45,156, inda 68,166 (71.635) suka samu akalla credit 5 ciki har da darussan Lissafi da harshen Ingilishi.

Farfesa Wushishi ya ce, dalibai 82,082 (86.26%) kuma sun samu akalla Credit biyar, ba tare da la’akari da darussan lissafi ko Ingilishi ba.

An samu dalibai 9,016 (31.7%) da laifukan satar jarabawa, wanda ya haura mutum 6,160 da aka samu a 2024.

Farfesa Wushishi ya kara da cewa  masu kula da jarrabawa biyar kuma—biyu daga Babban Birnin Tatayya da kuma daya kowanne a jihohin Kano, Adamawa da Ondo—an kama su da laifin taimaka wa satar jarabawa.

Za kuma a soke lasisin cibiyoyin jarrabawa hudu, biyu a jihar Neja da kuma daya a jihohin Yobe da Kano saboda samun su da laifin taimaka wa satar jarabawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *