• Home  
  • Gwamnatin Kano ta ware naira miliyan 99 domin rigakafin cutar mahaukacin kare
- Babban Labari - Labarai

Gwamnatin Kano ta ware naira miliyan 99 domin rigakafin cutar mahaukacin kare

Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan 99 domin fara shirin rigakafin cutar mahaukacin kare (rabies), inda ake sa ran yi wa akalla karnuka 10,000 allurar rigakafi a mataki na farko. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktar Wayar da Kai ta Ma’aikatar Raya Dabbobi ta jihar, Halima Gadanya, ta […]

Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan 99 domin fara shirin rigakafin cutar mahaukacin kare (rabies), inda ake sa ran yi wa akalla karnuka 10,000 allurar rigakafi a mataki na farko.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktar Wayar da Kai ta Ma’aikatar Raya Dabbobi ta jihar, Halima Gadanya, ta fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ne ya bayar da amincewar a matsayin wani bangare na kokarin gwamnatinsa na kare lafiyar al’umma daga cututtukan da ake iya kauce musu amma masu hadari.

Shirin zai kasance karkashin jagorancin Ma’aikatar Raya Dabbobi ta jihar, inda kwamishinan ma’aikatar, Aliyu Isah Aliyu, zai kula da aiwatar da shi kamar yadda jaridar Punch ta ambato.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai