Wata cibiya mai lura da harkokin aikin Hajji da Umara da ke kasar Ingila ta bai wa Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, takardar shedar kwarewa kan jagoranci da tafiyar da harkokin Hajji da Umara.
An ba shi takardar shaidar ne bayan kammala wani shirin musayar bayanai da kara wa juna sani a matakin kasa da kasa da aka gudanar domin inganta tafiyar da harkokin aikin Hajji da Umara a tsakanin kasashe daban-daban.
Shirin ya hada manyan masu ruwa da tsaki da jami’an da ke kula da harkokin aikin Hajji daga kasashe daban-daban, inda suka tattauna kan hanyoyin da za su inganta kula da alhazai tare da kara ingancin ayyukan da ake yi musu a lokacin gudanar da ibadar Hajji da Umara.
Takardar shaidar ta nuna amincewa da irin kwarewar jagoranci da kokarin da Alhaji Ahmed Umar Labbo ke yi wajen inganta harkokin gudanar da aikin Hajji da Umara a Jihar Jigawa.
Jami’in hulda da Jama’a na hukumar Habib Yusuf Adamu Babura ya bayyana cewa wannan takardar shedar ta zo ne sakamakon tattaunawa da musayar kwarewa tsakanin hukumomin da ke kula da aikin Hajji a kasashe daban-daban, musamman kan batutuwan da suka shafi kula da jin dadin alhazai, shirye-shiryen tafiya, da kuma inganta ayyukan da ake yi wa maniyyata.
Kara karantawa: jig
Haka kuma, an bayyana cewa wannan shi ne karon farko da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta samu irin wannan takardar sheda daga wata cibiya ta kasa da kasa kan jagoranci da tafiyar da harkokin Hajji da Umara.
Masu sa ido kan harkokin Hajji sun ce wannan nasara na nuni da yadda hukumar ke kokarin tafiyar da ayyukanta bisa ka’idojin kasa da kasa, tare da kara inganta ayyukan da ake yi wa alhazan jihar.
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ce ke da alhakin shirya dukkan harkokin aikin Hajji ga alhazan jihar, ciki har da rajista, shirye-shiryen tafiya, da kula da jin dadinsu tun daga lokacin tafiya har zuwa dawowarsu gida.
Ana sa ran wannan karramawa za ta kara karfafa gwiwar hukumar wajen inganta ayyukanta domin tabbatar da samun nasarar gudanar da aikin Hajji ga alhazan Jihar Jigawa a nan gaba.
